Labaran Wasanni
Lewandowski ya lashe kyautar dan wasa mafi zura kwallaye a Turai
Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich, Robert Lewandowski ya lashe takalmin zinare a matsayin wanda ke kan gaba da yawan cin kwallaye a nahiyar Turai a kakar wasanni ta shekarar 2020/2021
Dan wasan dan asalin tawagar kasar Poland ya ci kwallaye 41 a kakar Bundesliga da ta gabata, inda ya zama na 2 dake taka leda a kasar Jamus daga waje da ya karbi kyautar bayan bajintar da dan wasa Gerd Muller ya yi na cin kwallaye 40 a shekarar 1970 da kuma a 1972.
Aisha Buhari Cup: Banyana-Banyana ta doke Super Falcons a wasan karshe
Lewandowski ya karbi kyautar takalmin zinaren daga hannun Ciro Inmobile, wanda ya zama zakara a kakar wasanni ta shekarar 2019/2020 a bikin da rukunin European Sports Media ke gabatarwa tun daga 1968, in banda 1990 da aka ci karo da cikas.
Bayan Muller an samu fitattun ‘yan wasan kwallon kafa da suka ci kyautar da suka hadar da Lionel Messi da Cristiano Ronaldo da Francesco Totti da Thierry Henry da Ronaldo da Marco Van Basten da Hristo Stoichkov da kuma Eusebio.
You must be logged in to post a comment Login