Kiwon Lafiya
Libiya ta dawo da yan Najeriya 136 filin jirgin saman jihar Lagos
Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA ta sake karbar ‘yan Najeriya 136 daga kasar dake zaune a kasar Libiya da suka yi carko-carko a can.
Jami’in dake kula da shiyyar Lagos Alhaji Idris Muhammed ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai da safiyar yau Talata.
Alhaji Idris Muhammed ya kara da cewar ‘yan Najeriya sun sauka a filin jirgin saman Murtala Muhammed dake Lagos da misalin karfe 11 da minti 50 na daren jiya Litinin cikin jirgin saman Al-Burka mai lamba MJI.
A cewar babban jami’in an dawo da ‘yan gundun hijira ne tare da hadin gwiwar hukumar kula da bakin haure ta duniya da kungiyar tarayyar Turai tare tallafin shirin dawo da bakin haure na ‘yan sa kai AVR, wadanda suke taimakawa bakin haure dawo kasar su ta haihuwa.
Daga cikin wadanda aka dawo da su gida Najeriya akwai mata matasa 59 da jarirai 5 da kuma kananan yara 4.
Sauran su ne maza 63 da kananan yara 5.