Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Libya Football: Ali El Margini ya ajiye aiki

Published

on

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta kasar Libya Ali El Margini ya ajiye aikinsa bayan da kungiyar ta yi rashin nasara a wasanni uku da ta buga.

El Margini ya fara aikin horas da kungiyar a watan Satumba da ya gabata tun a lokacin dai Libya ta yi rashin nasara a wasan sada zumunta da Comoros sai kuma wasanni biyu da Equatorial Guinea a yayin neman tikitin gasar cin kofin Afrika.

Rashin nasarar da Libya ta yi a wasannin ya sanya kasar zuwa na karshe a rukunin J da maki uku, inda kasar Tanzania ke gabanta da maki hudu sai Equatorial Guinea da shida yayin da kuma Tunisia ta yi nasarar samun tikitin zuwa gasar a kakar wasa mai zuwa.

El Margini ya ce “Yanayin da kungiyar ta samu kanta a ciki tare da annobar cutar COVID-19 da kuma rikicin siyasa a kasar ne suka sanya lalacewar ‘yan wasan.”

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!