Connect with us

Labaran Wasanni

PSG na bukatar Neymar da Mbappe su kara mata kwantiragi

Published

on

Daraktan wasanni na kungiyar kwallopn kafa ta PSG Leonardo, ya ce, sun fara tattaunawa da ‘yan wasansu Neymar da Kylian Mbappe kan batun kwantiraginsu da kungiyar.

‘Yan wasan gaban guda biyu wadanda PSG ta kashe sama da Yuro miliyan 400 wajen daukosu, kwantiragin na su zai kare a shekarar 2022.

Leonardo ya kuma ce, suna cigaba da tattaunawa batun kwantiragin Angel Di Maria da kuma Juan Bernat.

Haka zalika ya bayyana cewa za a kawo karshe duk wani batu na tsawaita kwantiragin wasu daga cikin ‘yan wasan kungiyar a mako mai kamawa.

Daraktan ya ce “Akwai kyakkyawar alaka tsakani na da Thomas Tuchel don haka bana tinanin canjashi duk da rashin nasarar da muka samu a wasanni biyu cikin uku na farko a gasar Champions League.”

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,910 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!