Labaran Kano
Likitoci sun gano abinda ke janyo ciwon hauka
Wani bincike da likitocin kwakwalwa suka gudanar ya gano cewa, cutar damuwa watau Depression shi ne kan gaba wajen sanya mutane na kamuwa da ciwon Hauka.
Wata ma’aikaciya a asibitin kula ma masu lalurar kwakwalwa na Dawanau da ke nan Kano Hajiya Amina Idris Muhammad ce ta bayyana hakan ta cikin shirin ‘’Barka da Hantsi’’ nan Freedom Radio.
Ta ce cutar ta damuwa na jefa mutane cikin larurori da dama inda take kama mutane sakamakon sanya yawan damuwa a ransu bisa wani abu da ya sha musu kai.
Haka kuma ta kara da cewa, matasan wannan yanki na Arewacin Najeriya na fama da yawan tunane-tunanen al’amuran yau da kullum wanda hakan ke sanya su fadawa cikin wannan matsala.
Da yake nasa jawabin, Malam Nura Husain wanda shi ma ya kasance a cikin shirin, ya bayyana cewa a matsayinsu na masu kula da masu lalurar kwakwalwar, suna fama da matsalar rashin baiwa marasalafiyar magungunansu yadda ya kamata har ma da rashin mayar da su asibitin akan lokaci.