Labarai
Likitoci sun rasa rayukan su saboda zargin kamuwa da zazzabin Lassa
Ana zargin cewar, likitocin sun kamu ne da cutar sakamon duba wata mace mai juna biyu da ta zao daga jihar Bauchi.
A wata ganawa da darakatan kula da lafiyar alumma na ma’aikatar lafiya na jihar Kano Dr, Imam Wada Bello ya tabbatar da afkuwar al’amarin cewar likita guda da yake neman kwarewa da kuma wata mace guda.
Likitoci dai 2 sun rasu Jim kadan Bayan yiwa wata marar lafiya tiyata a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano.
Daga bisani galiban ma aikata da suka taimaka wajen yiwa marar lafiyar tiyata sun kamu da wani zazzafan zazzabi wanda har yanzu aka kasa Gano kansa.
Wannan dai yasa an fara zargin yiwuwar samun barkewar zazzabin Lassa, Koda yake mahukuntan asibitin na Malam Aminu Kano sunce sun aika da jinin wadanda ake zargin sun yi mu’amalla da marar lafiyar wacce tuni itama ta rasu, zuwa Lagos domin yin gwaji a tabbatar da matsayin irin wannan zazzabin da ake zargin na Lassa ne.
Dan haka ake kira ga al’umma da su kiyaye tsaftar muhalli.