Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Likitoci za su fara yajin aikin sai baba ta gani a Najeriya

Published

on

Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta kasa NARD za ta fara yajin aiki a fadin Najeriya daga ranar 31 ga watan Maris din nan, wanda shi ne na uku a cikin watanni 9.

Kungiyar ta koka kan rashin biyan alawus din mambobinta, da kuma jan kafar da gwamnatin tarayya take yi wajen cika alkawuran da ta daukarwa mambobin kungiyar.

Wata sanarwar hadin gwiwa mai kwanan watan 18 ga Maris din nan da kungiyar ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta Dr Uyilawa Okhuaihesuyi da sakatarensa Dr Jerry Isogun, ta bukaci likitocin su zauna cikin shirin tafiya yajin aikin daga ranar 31 ga watan nan na Maris da muke ciki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!