Kiwon Lafiya
Likitoci:Yawan shan Paracetamol ba bisa ka’ida ba ka iya haifar da ciwon Koda
Kungiyar masana kan magunguna ta kasa tayi gargadin cewa yawan mafani da maganin zazzabi na Paracetamol ba bisa ka’ida ba, ka iya haifar da ciwon koda ko kuma hanta.
Shugaban kungiyar shiyyar birnin tarayya Abuja mista Jelili Kilanine ya bayyana hakan yayin wata ganawar sa da manema labarai a birnin tarayya, inda ya jaddada cewa akwai bukatar mutane su rika bin dokokin da likitoci suka gindaya musu wajen amfani da maganin.
Mista Jelili ya lura da cewa mutane sukan yi gaban kan su wajen amfani da maganin zazzabin na Paracetamol, kuma yin hakan babbar barazana ce ga rayuwar su.
Ya kara da cewa wasu mutanen kan wuce kima wajen shan maganin, duk da nufin samun sauki cikin kankanin lokaci, wanda kuma yin hakan a cewar sa ba dai-dai bane.
Mista Kilani ya kuma bukaci al’ummar kasar nan da su nesanta kawunan su daga aikata wannan danyan aikin, kasancewar hakan babbar barazana ce ga lafiyar su.