Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

‘Yan Najeriya da dama na dauke da cutar Hanta – Jami’ar Jos

Published

on

Asibitin koyarwa na Jami’ar Jos ya ce a cikin mutane dari dake kasar nan mutun ashirin daga cikin su na dauke da ciwon hanta ba tare da sun san hakan ba.

Shugaban Asibitin koyarwa na Jami’ar ta Jos Farfesa Abraham Orkurga Malu, ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi kan irin hanyoyin da mutane za su bi dan kare kansu daga kamuwa da ciwon hanta.

Farfesan ya bayyana hakan ne a  wani taro  wanda  Asibitin Aminu Kano tare da  hadin gwiwa da Jami’ar Bayero suka shirya dan karrama Farfesa Musa Muhammad Borodo game da kan mukamin da ya samu na shugabantar kwalejin horas da likitoci ta kasa, da ya samu halartar manyan likitoci da dama daga kasar nan.

Likitoci:Yawan shan Paracetamol ba bisa ka’ida ba ka iya haifar da ciwon Koda

Wasu magungunan kwari da manoma ke amfani da su na da illa ga lafiyar dan Adam

Farfesa Abraham Orkurga Malu, ya yi kira ga al’umma da su dinga zuwa asibiti gwajin  lafiyar su don tantance cewar  ko suna dauke da cutar ko akasin haka  dan basu shawarwarin  hanyoyin matakan kariya.

A nasa jawabin a  taron shugaban Asibitin Aminu Kano Farfesa Abdurrahman Abba Sheshe,  yace zabar Farfesa Borodo, a matsayin shugaban kwalejin horas da likitoci na kasa zai taimakawa cigaban lafiya musamman dan dakile cutar hanta a kasar nan.

Shi kuma daga banagren sa, shugaban sashen da aka karrama Farfesa Muhammad Borodo, ya sha alwashin ci gaba da horar da kwararrun likitoci a kasar nan dan inganta harkokin lafiya.

A karshe Farfesa Abraham Orkurga Malu yayi kira ga shugabannin siyasa dana addinai da kungiyoyi masu zaman kansu da dai-daikun mutane su bada gudunmowar su  wajen magance yawaitar cutar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!