Labarai
Limami: Sakacin koyarwar addinin musulinci shike kawo annoba
Limamin Masallacin Juma’a na Jami’u Ibadurrahaman dake Unguwar Tudun Yola cikin karamar Hukumar Gwale a nan Kano, Malam Muhammad Sani Zakariyya ya bukaci al’ummar musulmi dasu dage wajen riko da koyarwar Addinin musulunci a dukkan ayyyukan su na yau da kullum.
Muhammad Sani Zakariyya ya bayyana haka ne a yayin Hudubar Sallar Juma’a da ya gabatar a Masallacin dake Unguwar ta Tudun Yola.
Limamin ya kuma ce ganin irin abubuwan da suke faruwa a duniya na barkewar cututtuka alamu ne na sakacin mutane wajen riko da koyarwar Addini yadda ya kamata.
Shi ma da yake jawabi shugaban majalisar Malamai ta kasa reshen Jihar Kano, Malam Ibrahim Khalil ya ce a wajen al’ummar musulmai, barkewar annoba ba wani sabon abu bane da al’umma za su tayar da hankalin su a kai, yana mai cewa ko a cikin al’qur’ani mai girma sai dai Al.. S. W.T ya yi Magana akan jarrabar al’ummar musulmai.
Wadansu magidanta sun karbi Musulunci a garin Sumaila
Malam Ibrahim Khalil ya kuma ce abinda ya kamata al’umma su mai da hankali shi ne yawan sadaka da taimakawa marasa karfi tare da yawaita tuba.
Wakilin mu Bilal Nasidi Mu’azu ya ruwaito cewa limamin masallacin ya kuma bukaci hukumomi da sauran al’umma da su rage yada labarin da ya shafi cutar mai makon haka su mayar da hankali wajen baiwa al’umma shawarwari akan matakan kariya.
You must be logged in to post a comment Login