Labarai
Lokaci ya yi da matasan Afrika za su fara yin jagoranci- Obasanjo

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, ya jaddada buƙatar cewar lokaci ya yi da matasan Afrika zasu fara riƙe muƙaman jagoranci a faɗin nahiyar.
Ya bayyana hakan ne a yayin taron wayar da kan mtasaka kan shugabanci mai taken Presidential Youth Mentorship Retreat da aka gudanar a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun, ƙarƙashin cibiyar ci gaban Matasa a Ɗakin Tarihi na Shugaba Olusegun Obasanjo OOPL.
Tsohon shugaban ya jaddada cewa lokaci ya yi da matasa za su tashi tsaye su jagoranci nahiyar Afrika domin makomarsu ta dogara da abin da suka yi a yau.
Ya yin taron, tsohon Babban Hafsan Tsaron kasar nan , Janar Martin Luther Agwai mai ritaya, ya ce barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya, ya zama gargaɗi ga shugabanni su ƙara ƙaimi wajen yaƙi da rashin tsaro.
You must be logged in to post a comment Login