Labarai
Ma’aikatan wucin gadi na INEC sun koka kan kin biyansu kudin aikin zabe
Wasu ma’aikatan wacin gadi a hukumar INEC da suka gudanar da aikin zaben bana, sun bukaci mahukunta da su shiga lamarinsu, wajen ganin an biya su hakkin su na aikin zabe da suka yi.
A zantawar Freedom Radio da ma’aikatan sun shaida mata cewa har ‘kawo yanzu an gaza biyansu hakkokin su, duk da irin zarya da suke yin a ganin hakkin su ya fito’.
Wadanda suka ce ‘kamata yayi ya zuwa yanzu hukumar INEC din ya kamata ace ta biyasu kudin aikin su, sai dai abin takaicin idan suka je neman hakkin nasu ko ofishin INEC din ba’a barinsu su shiga, jami’an tsaro suke koro su tun daga kofar shiga, tare da yi musu barazana zasu yi musu feshin ruwan zafi idan basu bar wurin ba’.
Wasu daga cikin su kuwa cewa sukayi ‘ko kudin aikinsu na zaben shugaban kasa INEC din bata biya su ba, bare na baya-bayan nan da akayi’.
Kan koken nasu ne Freedom Radio ta tuntubi mai magana da yawun hukumar INEC a nan Kano Ahamd Adam Maulud, don jin inda aka kwana kan batun hakkin nasu.
‘Sai dai ya ce kofar hukumar tasu a bude take, a don hakan kowanne lokaci zasu iya kai koken nasu INEC din, duk da bai bari an nadi muryarsa ba’.
Rahoton: Usaina Isma’il Rano
You must be logged in to post a comment Login