Labarai
Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya ta yi gargaɗi kan samun ambaliya

Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya ta sake yin sabon gargaɗi kan yiwuwar samun ambaliya Ruwa a wasu jihohi.
A wata takarda da Daraktan Sashen kula da Kwazazzabai da Ambaliya da yankunan gaɓar Ruwa, Alhaji Usman Abdullahi Bokani, ya sanya wa hannu, aka rabawa manema labarai an bayyana cewa ana sa ran ruwan sama mai yawa tsakanin 1 zuwa 3 ga watan Oktoba, 2025, wanda ka iya haddasa ambaliya.
Jihohin da ambaliyar ka iya shafa sun haɗa da Adamawa, Kebbi, Bauchi, Zamfara, Sakkwato, Kaduna da Neja, inda a jihar ta Kebbi ake tsammanin samun ambaliyar garuruwan Argungu, Bagudu, Gwandu, Jega, Kalgo, Kamba, Kangiwa da Birnin Kebbi.
Sai jihar Kaduna dake da yankin Jaji da Zariya kawai, yayin da a Jihar Neja ake tsammanin samun hakan a Magama da Sarkin-Pawa, sai garuwan Mubi, Gusau da Azare dake jihohin Adamawa da Bauchi da Zamfara.
Ma’aikatar , ta shawarci jama’a da ke zaune kusa da koguna ko rafuka su ɗauki matakan kariya ko su bar waɗannan wurare domin guje wa ambaliyar.
You must be logged in to post a comment Login