Labaran Kano
Ma’aikatar Shari’a ta Kano ta musanta rahoton sakin Alasan Ado Doguwa

Ma’aikatar Shari’a ta jihar Kano, ta musanta rahoton cewa Kwamishinan Shari’a yana shirin yin amfani da damar da yake da ita wajen sakin Alhassan Ado Doguwa.
Mai gabatar da ƙara a Shari’ar kuma Lauyan Gwamnati Barista Lamiɗo Abba Soron Ɗinki ne ya musanta batun a zantawarsa da Freedom Radio.
Lauyan ya ce, za a tabbatar da cewa an yi adalci a shari’ar kamar yadda ake yi wa duk wanda ake zargi da aikata kowanne irin laifi.
You must be logged in to post a comment Login