Labaran Wasanni
Mafarki na ya tabbata- Ighalo
Sabon dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Odion Ighalo, ya ce mafarkin sa ya tabbata na kasancewa dan wasan kungiyar Manchester United, domin abu ne da ya jima ya na burin ya tabbata.
Ighalo ya bar kasar Sin zuwa Manchester a jiya lahadi, bayan ya bar kungiyar Shanghai Shenhua dake kasar ta Sin.
Dan wasan mai shekaru 30 da haihuwa tsohon dan wasan kungiyar Watford kuma tsohon dan wasan Nijeriya, ya ce ya dade ya na burin kasancewar zama dan kungiyar Manchester, sannan ya shiga kungiyar ta Old Trafford, inda ya maye gurbin dan wasa Marcus Rashford wanda ya samu rauni.
Ighalo ya kuma ce abun farin ciki ne wanda ya jima ya na son ganin kansa a wannan kungiya tun ya na yaro, a lokacin da yake zantawa da tashar Sky sports bayan da ya sauka a kungiyar Manchester.
Ya ce ya na cike da farin cikin samun kansa a kungiyar, a cewarsa wata babbar dama ce a gare shi.
Tun da farko dai Ighalo ya ki karbar tayin wasu kungiyoyin wasan kwallon kafa ne inda ya zabi bangaren mai horaswa Ole Gunnar Solskjaer wato karbar tayin kulub din na Manchester.
Dan wasan dai ya jefa kwallo 16 a wasanni 55 na gasar premier ga kungiyar Watford kafin ya bar kungiyar inda ya koma Changchun Yatai a Junairun 2017 inda ya koma kungiyar Shanghai Shenhua na tsawon shekaru biyu.