Connect with us

Labaran Wasanni

Shin Ko Ighalo ya fi Hazad da Jovic?

Published

on

Tsohon Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles Odion Ighalo ya zama wani tauraro da kafafen yada labarai a baya bayannan da ake magana akanshi sakamakon namijin kokari da ya ke yi a sabuwar kungiyarsa da ya sauya sheka a matsayin aro wato Manchester United.

Odion Ighalo dai i zuwa yanzu, ya zura kwallaye uku a wasa uku da ya yi ga Manchester United tun bayan sauya shekarsa lamarin da masu sharhin kwallon kafa ke ganin cewa ya taka rawar gani sosai musamman idan aka yi la’akari da cewa Shekarun sa sun ja sosai.

Wasu na ganin cewa dauko Ighalo da mai horas da kungiyar Manchester United Ole Gunner Solksjaer ya yi ba karamar dabara bace kasancewar ya same shi a bagas ba tare da kashe kudade masu yawa ba.

A bangare guda akwai masu ikirarin cewa Odion Ighalo ya fi ‘yan wasa biyu da kungiyar Real Madrid ta kashe makudan kudade da suka kai fam miliyan dari da sittin wajen sayo su.

Wadannan ‘yan Wasa dai da ake magana akansu sune: Eden Hazad wanda ya sauya sheka daga kungiyar Chelsea zuwa Madrid akan kudi fan miliyan dari (100), da Kuma Luka Jovic wanda ya koma kungiyar ta Real Madrid daga kungiyar Benfica akan kudi fan miliyan sittin (60).

‘Yan wasan biyu dai gaba dayansu a bana, sun yi wasannni talatin da (33), sun kuma zura kwallaye uku kacal yayin da a nashi bangaren Odion Ighalo a wasa biyu kawai da aka fara da shi, ya zura kwallaye uku.

Wannnan dai shi ya sa masana harkokin wasanni ke ganin Real Madrid ta yi asarar kudaden ta ne wajen sayo wadannan ‘yan wasa biyu.

Yayin da a nata bangaren Manchester United ta tsinci dami a Kala.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,845 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!