Labarai
Magance matsalar yunwa da rashin aikin ne kadai hanyar magance matsalar mayakan Boko Haram-Obasanjo
Tsohon shugaban Najeriya chief Olusegun Obasanjo ya ce ta hayar magance matsalar yunwa da rashin aikin yi a kasar za’a iya magance matsalar mayakan kungiyar Boko Haram.
Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne a garin Maidugurin jihar Borno lokacin da ya ke jagorantar taron shirin kawar da yunwa wanda ya hadar da gwamnatin tarayya da kuma kungiyoyin kishin al’umma a fadin duniya.
Obasanjo ya ce bincike ya nuna cewar mafiya yawan mayakan boko haram ba wai sun dauki makami ne domin ya ki da kasa ba ko kuma ciyar da wani addini gaba sai dai don su yaki yunwa da kuma rashin aikin yi.
Shi dai Obasanjo shi ne ke jagorantar shirin muradan karni wanda ke kula da yaki da yunwa a Najeriya, inda kuma yake jagorantar gangamin yaki da yunwar a wasu sassan kasar nan
Ya kuma ce manufofin shirin muradan karni guda goma 17 a kasashen duniya, yaki da yunwa shi me na biyu.