Labarai
maganin ciwon ido ya haddasa amai da gudawa a kano
Wasu Mutane da dama sun kamu da cutar Amai da Gudawa da matsanancin Ciwon ciki da Kumburin jiki a garin Panda dake yankin karamar Hukumar Albasu a nan Kano, sakamakon shan wani magani da mahukuntan karamar hukumar suka raba musu da zummar magance cutar Dundumi da yanar ido.
Rahotanni sun bayyana cewa wadanda suka kamu da cutukan sun hadar da al’ummar yankin Panda Tsohuwa da Shashiwai da kuma Panda Gandu.
Wasu daga cikin wadanda abun ya shafa sun ce an kawo musu maganin ne har gidajensu don ya yi musu maganin cutar Dundumi da kuma yanar idanu, sai dai shan maganin ya zame musu lalura, kamar yadda wata mata mai suna Rahina ta fada wadda ta ce, shan maganin ya haddasa mata ciwon ciki, gudawa da kuma ciwon kafa.
Wata matar Aure mai suna Rashida ta ce shan maganin ya haddasa mata Tari da Gudawa da kuma dashewar Murya, ita ma wata mai suna Halima ta bayyana cewa shan maganin ya haddasa mata Ciwon Ciki da amai.
Malam Ibrahim Sabo Muhammad shi ne Dagacin garin na Panda ya shaida wa Freedom Radio cewa shugaban sashen lafiya na karamar hukumar ne ya tara dagatai a gaban Hakimin karamar Hukumar aka sanar dasu cewa za’a kawo musu wannan magani domin rabawa mutane, wanda suka kawo maganin kuma dama sun sanar da mutane idan aka sha maganin za’a iya yin Amai ko Gudawa ko kuma Ciwon ciki.
Sai ko da Freedom Radio ta tuntubi shugaban Karamar Hukumar ta Albasu Ibrahim Turaki Faragai, ya ce bai san da matsalar ba, amma tunda yanzu an sanar da shi zai gudanar da bincike kan lamarin.