Labaran Wasanni
Magoya bayan Manchester United na fatan a sallami mai horar da kungiyar kafin wasan Tottenharm

Wasu magoya bayan kungiyar kwallon kafa na Manchester United sun ce suna fatan hukumar gudanarwar kungiyar za ta Kori mai horar da ita Ole Gunnar Solskjær sakamakon rashin a bin a zo a gani a ƙungiyar ke yi.
A baya bayannan dai Manchester United ta yi rashin nasara a hannun Liverpool da ci 5-0 a filin wasanta na Oldtrafrod.
A cewar su kafin wasanni 2 masu zafi da kungiyar za ta kara nan gaba da Tottenham da kuma kungiyar Manchester city ya kamata a sallameshi.
A na ganin cewa mai horos da Manchester United bazai iya tsallake wasannin da zai fafata ba da kungiyoyin guda biyun ba.
You must be logged in to post a comment Login