Manyan Labarai
Majalisa dokoki ta Kano ta sake zama tun bayan dage dokar kulle
Majalisar dokoki ta jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar Kano kan ta kai wa al’ummar garin Yaryasa a karamar hukumar Tudun wada da wasu garuruwa da ke makwabtaka da garin daukin gaggwa sakamakon Ambaliyar ruwa da ta haddasa zaizayar kasa a yankunan.
Bukatar hakan ya biyo bayan kudirin gaggawa da Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Tudun-wada Abdullahi iliyasu Yaryasa ya gabatar gaban zauren majalisar a zamanta na yau Litinin.
Da yake gabatar da kudirin Abdullahi iliyasu Yaryasa, ya ce, yanzu haka akwai mutane da dama da sanadiyyar ambaliyar ruwan ta tilasta musu barin gidajensu.
Haka dai a zaman majalisar na yau, shi ma mamba mai wakiltar kananan hukumomin Rimin Gado da Tofa Muhammad Bello Butu-butu, ya gabatar da kudirin gaggawa kan neman gyara wasu manyan gadoji biyu da lalacewarsu ta jefa al’ummar da yake wakilta cikin mawuyacin hali.
Haka kuma Muhammad Bello Butu-butu, ya kara da cewa, al’umma da dama ne ke amfani da gadojin wadanda lalacewar da suka yin ta sanya mu’amala da sauran harkokin yau da kullum suka yi tsauri a yankunnnan.
Wakilinmu na majalisar dokokin ta jihar Kano Auwal Hassan Fagge, ya ruwaito mana cewa, dan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Dawakin Tofa Sale Ahmad Marke yayin goyon bayan kudirin na dan majalisar mai wakiltar Tudun wada, ya ce ya kamata a kaiwa mutanen dauki da gaggawa domin kuwa idan aka tsaya jan kafa dab ambaliya take da shafe garin baki daya.
You must be logged in to post a comment Login