Labarai
Majalisa ta buƙaci gwamnati ta sanya CCTV a babban Masallacin Kano
Majalisar dokokin jihar Kano, ta buƙaci gwamantin jihar da ta gyara Babban masallacin Kano tare da sanya masa kyamarorin tsaro na CCTV domin tabbatar da tsaro a ciki da wajensa har ma da wasu sassan ƙaramar hukumar Birni.
Majalisar ta buƙaci hakan ne sakamakon kuɗurin da ɗan majalisa mai wakiltar Karamar hukumar Birnin Yusuf Aliyu Daneji, ya gabatar yayin zaman ta.
Yayin da ya miƙe domin gabatar da wannan ƙuduri, ɗan majalisar ya ce, a kwanakin baya wasu ɓata garin matasa su fiye da 50 sun je masallacin inda suka ɗaure masu gadi tare da yin awon gaba da na’urorin sanyaya masallacin.
Haka kuma ya ƙara da cewa, bayan kwanaki kaɗan ɓata garin sun sake komawa masallacin tare da sake yin wata satar.
“Don haka wannan masallaci mai matuƙar daraja da tarihi ya na buƙatar waɗannan na’urori domin tabbatar da tsaro” inji Yusuf Aliyu Daneji.
You must be logged in to post a comment Login