Labaran Kano
Majalisa ta janye dakatarwar da Kansilolin suka yi wa shugaban karamar hukuma
Majalisar dokokin jihar Kano, ta janye dakatarwar da Kansilolin Karamar hukumar Nassarawa suka yi wa shugaban karamar hukumar Auwalu Lawan Shu’aibu Aramfosu.
Majalisar ta dauki matakin ne biyo bayan takardar da Kansilolin suka aike mata suna masu sanar da dakatar da shugaban karamar hukumar sakamakon zarginsa da badakalar kudi, inda shi ma ya aike wa majalisar wasikar koke ya na mai musanta batun tare da cewa ya samu rahoton dakatarwar a kafafen sada zumunta.
Bayan karanta wasikar ne a zaman majalisar na yau Litinin, ta dauki matakin cewa dakatarwar ba ta kan doka, don haka ta umarci kwamitinta ba harkokin kananan hukumomi da masarautu kan ya gudanar da bincike kan batun tare da gabatar da rahotonsa nan da mako guda kamar yadda shugaban majalisar Jibril Isma’il Falgore, ya sanar.
Majalisar, ta kuma karanta wasikar da babban Mai binciken kudi na Kano ya aike mata mai ɗauke da bayanan kuɗaɗen da gwamnati ta kashe a bara.
You must be logged in to post a comment Login