Labarai
Majalisa:An samu hargitsi yayi gabatar da kunshen kasafin kudin badi
A jiya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kudirin kunshin kasafin kudin badi da haura Naira tiriliyon 8 ga zauren majalisar dokoki ta kasa.
An sami bambaci tsakanin kasafin kudin wannan shekarar da muke ciki da Naira biliyan dari 300 cikin Kunshin kasafin kudin badin, kamar yadd aka aiwatar
Muhimman bangarori da kasafin ya kunsa, sun hada da gebewa bangaren man fetur Naira biliyan 305 wanda za’a baiwa babban kamfanin mai na kasa NNPC yayin da za’a kashe wajen biyan rarar man fetur.
A cewar, shugaban kasa Muhammadu Buhari kundirin kasafin kudin badin na san ran za’a sami kudaden shiga fiye da Naira biliyan 6 yayin da aka sami bambanci fiye da Naira tiriliyan 7 idan aka kwatanta da na bana, bayan da aka sami gibin fiye da Naira biliyan guda.
Alamu sun nuna cewar, gwamnati mai ci ta yi alkwarin zata kudaden da take kashewa a manyan ayyukan yayi kasa da fiye da Naira tiriliyan 2 idan aka kwatanta da na bana da kuma na badin.