Kiwon Lafiya
Majalisar dattawa ta bukaci kwamitinta ta yi binciken kashe-kashen jihar Benue
Majalisar Dattawa ta bukaci kwamitinta na musamman da ke bincike kan kashe-kashen da suka faru a jihar Benue da ya gabatar da sakamakon binciken-sa a Talatar makon gobe.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ofishin shugaban majalisar Dattawa sanata Bukola Saraki ya fitar da yammacin jiya a Abuja.
Sanarwar ta ce; kashe-kashen da ke faruwa a jihar Benue abin takaici ne kuma ya nuna gazawa na jami’an tsaron kasar nan.
A cewar sanarwar, ganin munin lamarin ya sa a watan Nuwamban bara majalisar ta Dattawa ta kafa kwamiti mai karfi karkashin jagorancin shugaban masu rinjaye Sanata Ahmed Lawan wanda aka umurci kwamitin da ya yi aiki da jami’an tsaro domin gano matsalar