Kiwon Lafiya
Majalisar Dattawa zata binciki ma’aikatar kula da tallafin karatu bisa zargin badakalar kudade
Majalisar Dattawa tace zata binciki ma’aikatar kula da tallafin karatu ta tarayya kan zarge-zargen da ake mata na badakalar kudade da suka wuce kima.
Kwamitin majalisar Dattawan da ke sanya ido kan al’amuran asusun tallafawa manyan makarantun ne ya bayyana hakan, lokacin da hukumar gudanarwar ma’aikatar ke gabatar da kunshin kasafin wannan shekarar ta 2018.
Kwamitin karkashin jagorancin Sanata Jibrin Barau da ke wakiltar Kano ta arewa a zauren majalisar, ya bayyana takaicin sa kan yadda daraktar gudanarwar hukumar Fatima Ahmad ta gabatar da kasafin wannan shekarar, inda ya zargi jami’an hukumar na amfani da tallafin da take bawa daliban da ke karatu a kasashen ketare, wajen yiwa gwamnati badakalar kudade.
Kan wannan batu ne Sanata Jibrin Barau yace kwamitin majalisar zai gudanar da kwakkwaran bincike, domin bankado irin badakalar kudaden da hukumar takeyi, yayinda take fakewa da daliban da ta tura kasashen waje karatu.
Ya kara da cewa abin takaici ne ace ana badakalar miliyoyin kudade a hukumar, inda yace ba zasuyi kasa a gwiwa ba har sai sun bankado wadanda ke da hannu a badakalar da kwamitin ke zargin ana aikatawa a hukumar.