Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majalisar dattijai ta buƙaci Buhari ya ayyana ƴan bindiga a matsayin ƴan ta’adda.

Published

on

Majalisar dattijan ƙasar nan ta buƙaci shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ayyana ƴan bindiga a ƙasar nan a matsayin ƴan ta’adda.

Kazalika majalisar ta buƙaci shugaba Buhari ya ayyana shugabbanin ƴan ta’addar a matsayin waɗanda ake nema ruwa a jallo kuma waɗanda za a hukunta da zarar an kama su.

Wannan dai ya biyo bayan ƙudirin da sanata mai wakiltar Sokoto ta gabas Ibrahim Gobir da wasu sanatoci 8 suka gabatar.

Yayin da yake bada ƙudirin Gobir ya ja hankali majalisar kan wani harin ƴan ta’adda da suka kai shalkwatar tsaro ta Civil Depence da ke Sokoto a ƙarshen mako.

Har ma ya bayyana takaicin sa kan yadda harin yayi sanadiyyar mutuwar sojoji da ƴan sanda 16.

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!