Kiwon Lafiya
Majalisar Dattijai ta tunatar da hukumar INEC ikon da majalisar ke da shi
Majalisar Dattijai ta tunatar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC cewa kada fa ta manta da ikon da Majalisar ta ke da shi wajen yi wa dokar hukumar zabe ta shekarar2010 kwaskwarima.
Shugaban Majalisar Dattijan Sanata Bukola Saraki ne ya sanar da hakan lokacin da ya ke bude taron jin ra’ayin jama’a game da kudurin dokar samar da hukumar kula da laifuffukan da ake aikatawa lokacin zabe a jiya Litinin a Abuja.
Bukola Saraki ya buga misali da cece-ku-cen da gyaran fuskar da Majalisun Dokokin kasar nan su ka yi wa sashe na 25 na dokar zaben kasar nan, wanda ya sake fasalin babban zabe mai zuwa na shekarar badi.
Tun da farko INEC ta bayyana aniyarta ta kalubalantar gyaran fuskar a kotu amma daga bisani ta janye kudurinta.
A jawabinsa da ya gabatar shugaban INEC Farfesa Mahmoud Yakubu ya shaida cewa ya zuwa yanzu suna da Shari’u dubu daya da tamanin a gaban kotu, da suka shafi harkokin babban zaben shekarar 2015.
Shugaban Majalisar Dattijan wanda ya samu wakilcin mataimakin shugaban masu rinjaye na Majalisar Sanata Bala Ibn Na’All.. ya koka kan cewa wasu ‘yan-siyasar da ke da muradin tsayawa takara su ka fara yakin neman zabe tun kafin lokaci ya yi, a don haka ya bukaci INEC ta dauki matakin ladaftarwa a kansu.