Labarai
Majalisar dinkin duniya ta ce fiye da mutane miliyan daya ke mutuwa dalilin cutar tarin fuka
Majalisar dinkin duniya ta ce; mutane miliyan daya da dubu dari shida ne suke mutuwa duk shekara a dalilin cutar tarin fuka.
Ta kuma ce ba ya ga rasa rayukan, cutar za ta kuma janyo wa duniya asarar kudade dala tiriliyan daya kafin nan zuwa shekarar dubu biyu da talatin.
Sakatare Janar na majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ne ya bayyana haka, yayin wata ganawa da ya yi da wasu kungiyoyi masu zaman kansu a shalkwatar hukumar da ke birnin New York din kasar Amurka.
Ya ce dole ne al’ummar duniya su dunkule waje guda domin yakar cutar tarin fuka.
Sai dai ya ce; ba za a samu nasara ba matukar ba a dakile dalilan da suke ta’azzara cutar ba musamman talauci.