Labarai
Majalisar dinkin duniya ta nemi matasa su kasance masu neman na kai
Majalisar dinkin duniya ta bukaci matasa da su kasance masu neman na kansu hadi da jajircewa wajen neman ilimi da nufin inganta tattalin arzikin kasashen su.
Wannan na cikin wata sanarwa da majalisar ta sanyawa hannun a wani bangare na bikin ranar matasa ta duniya, da ake gudanarwa a yau Talata.
A cewar majalisar, matasa su ne kashin bayan kowacce al’umma baya ga lalubobo hanyoyin inganta rayuwarsu a nan gaba.
Akan kan ne wakilin mu Awwal Hassan Fagge ya jiyo ra’ayoyin wasu matasa a nan kwaryar birnin Kano, dangane da irin kalubalan da suke fuskanta.
Wani masanin nazarin hallayar dan Adam da ke Jami’ar Bayero a nan Kano, DR Abdullahi Mai Kano Madaki, ya bayyana hanyoyin da matasa za su bi don inganta rayuwarsa.
DR Mai-Kano Madaki ya kuma bukaci gwamnotoci a dukkannin matakai, da su kara kaimi wajen ciyar da matasa gaba a fannoni daban-daban na rayuwa.
Taken bikin na bana shi ne, hadin kan matasa don inganta rayuwarsu ta gaba.
You must be logged in to post a comment Login