Labarai
Majalisar ɗinkin duniya za ta magance ƙarancin abinci a Arewacin Najeriya
Majalisar ɗinkin duniya ta kafa kwamitin kar-ta-kwana da zai yi haɗin gwiwa da wasu ƙungiyoyin agaji don magance matsalar ƙarancin abinci a Arewacin Najeriya.
Babban Sakataren majalisar António Guterres, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun sa Stéphane Dujarric ta fitar.
António Guterres ya ce ƙungiyoyin da majalisar za su mayar da hankali ne, wajen ganin sun ƙara inganta harkokin noma a Najeriya ta yadda za’a magance fargabar da ake tunani na samun karancin abinci.
Sanarwar ta ce ƙungiyoyin za su yi aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin tarayya da kuma na jihohi domin ganin an samu nasara kan shirin da za a gudanar.
You must be logged in to post a comment Login