Ƙetare
Majalisar Dinkin Duniya za ta yi taron gaggawa bayan kifar da gwamnatin Syria
Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da taron gaggawa a yau Litinn domin tattauna batun faduwar gwamnatin shugaba Bashar al Assad na Syria, sakamakon hare-haren ba-zata daga ‘yan tawaye.
Kasar Rasha ce dai ta bukaci da a gudanar da wannan taro.
Shirya taron dai na zuwa ne bayan da wata kafar yada labarai a Moscow ta tabbatar da cewa Bashar al Assad, da iyalansa sun samu mafakar siyasa a kasar.
BBC ta ruwaito cewa, Amurka ce ke kan gaba wajen martani a game da hambarar da gwamnatin al Assad, inda shugaba Joe Biden, ya ce, faduwar gwamnatin al Assad wani muhimmin gishiki ne na adalci bayan shafe shekaru aru-aru na mulkin danniya, sai dai ya yi gargadin cewa kasancewar ‘yan tawaye ne suka kwace kasar akwai sauran barazana da rashin tabbas.
You must be logged in to post a comment Login