Labarai
Majalisar dokoki ta gayyaci Akpabio kan badakalar NDDC
Majalisar wakilai ta gayyaci ministan kula da yankin NIGER Delta Sanata Godswill Akpabio da ya gurfana gaban kwamitinta mai kula da yankin na Niger Delta don karin haske kan ayyukan hukumar ta NDDC.
Majalisar ta dau wannan mataki ne biyo bayan zarge-zarge da tsohuwar shugabar hukumar NIGER Delta Dr Joi Nunieh ta yi kan Mr Akpabio bayan da ta gurfana gaban kwamitin a yau.
A jiya Alhamis ne dai ‘yan sanda su ka yi yunkurin kama tsohuwar shugabar hukumar ta NDDC a gidanta da ke garin Fatakwal, kafin daga bisani gwamnan jihar Rivers Nyeson Wike ya ceto ta.
Wata majiya ta shaidawa manema labarai cewa watakila yunkurin kama da tsohuwar shugabar hukumar kula da yankin na Niger Delta yana alaka ne da yunkurin hanata halartar zaman da kwamitin kula da yankin na Niger Delta na Majalisar wakilai ke yi don gano gaskiyar zargin almundahana a hukumar
You must be logged in to post a comment Login