Connect with us

Addini

Sabawa ka’idar musulunci na taimakawa wajen tabarbarewar aure – Limami

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Millatu Ibrahim da ke unguwar Sauna Kawaji a nan birnin Kano, Malam Ali Dan Abba, ya ce, sabawa ka’idar musulunci ya yin neman aure da kuma rashin sanin hakkin juna na taka rawa wajen tabarbarewar zamantakewar aure musamman a tsakanin Hausawa.

Malam Ali Dan Abba ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala shirin “Barka da Hantsi” na nan tashar Freedom Radio da ya mai da hankali kan tabarbarewar zamantakewar aure a wannan lokaci.

Ya ce, matukar ma’aurata suka gaza sauke hakokin da ke tsakanin su musamman ma a bangaren namiji to kuwa zamantakewar aure zata samu tangarda.

Malam Ali ya kuma ce, ko da saki ya faru tsakanin ma’aurata, addinin musulunci ya bukaci dukkannin bangarorin biyu su kyautatawa juna.

Malam Ali Dan Abba ya kuma ce matukar aure aka dora shi a tafarki na kyale-kyale da rashin gaskiya to kuwa da zarar an fara zaman za a fuskanci sabani.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!