Labaran Kano
Majalisar dokoki za ta gyara dokar kafa hukumar samar da tallafin ilimi
Majalisar dokokin jihar Kano ta ce za tayi iya bakin kokarinta wajen tabbatar da gyaran dokar kafa hukumar bunkasawa da kuma samar da tallafi ga bangaren ilimi ta jihar Kano ta shekarar dubu biyu da goma sha tara wanda gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya turo da shi.
Mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kano Hamisu Ibrahim Chidari ne ya bayyana haka yayin karanta wasikar da gwamnan Kano ya turowa majalisar game da gyaran kudirin dokar hukumar ta Kano state education development establishment support bill 2019.
Ya ce matukar aka amince da gyare-gyaren da aka yi ga hukumar aka kuma amince da shi akan lokaci zai bai wa jihar Kano damar fara cin gajiyar tallafi kan harkokin ilimi daga kungiyoyin ba da tallafi kan harkar ilimi a duniya.
Wakilinmu na majalisar dokokin jihar Kano Abdullahi Isah ya ruwaito cewa, majalisar ta bukaci sanya batun gyaran dokar cikin ayyukan da za ta gudanar a zamanta na gaba.