Labarai
Majalisar dokokin jihar Katsina ta janye dokar karin wa’adin shekarun ritaya
Majalisar dokokin Jihar Katsina ta janye dokar nan da ta zartar ta karin wa’adin shekarun aiki kafin ritaya ga ma’aikatan majalisar daga shekaru 60 zuwa 65.
Haka zalika majalisar karkashin jagorancin shugabanta, Alhaji Tasi’u Maigari ta janye kudurinta na shekarun aikin daga shekaru 35 zuwa 40.
Matakin ya biyo bayan karbar rahoto na musamman kan shawarwarin gwamnan Jihar Aminu Bello Masari ya bayar game da kudurin gyaran dokar majalisar na shekarar 2021.
A baya dai majalisar dokokin Jihar Katsina ta amince da kara wa’adin shekarun aiki daga shekaru 30 zuwa 35, da kuma shekarun haihuwa kafin ritaya daga shekaru 60 zuwa 65.
You must be logged in to post a comment Login