Labarai
Majalisar Dokokin Kano ta amince da dokoki 2 da suka shafi inganta fannin lafiya

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da dokoki guda biyu da suka shafi inganta harkokin lafiya a jihar, bayan da suka tsallake karatu na biyu.
Dokar farko ta shafi tabbatar da ƙwarewa da horar da ungozoma na gargajiya domin ba su takardar shaidar aiki ta doka. Wanda hakan zai taimaka wajen rage mace-macen mata masu juna biyu da jarirai a yankunan karkara.
Haka kuma, majalisar ta karanta dokar kafa hukumar kula da dakunan gwaje-gwajen lafiya, wacce za ta tabbatar da ingantaccen binciken cututtuka da daidaita ayyukan dakunan gwaje-gwaje a fadin jihar.
Bayan karatu na biyu, kakakin majalisar, Alhaji Jibril Isma’il Falgore, ya tura dokokin zuwa kwamitocin da suka dace domin ƙarin nazari kafin amincewa da su gaba ɗaya.
You must be logged in to post a comment Login