Labarai
Majalisar dokokin Kano ta amince da gyaran dokar binciken kuɗin da gwamnati ke kashewa ta bana.
Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da gyaran dokar binciken kuɗin da gwamnati ke kashewa ta bana.
A Talatar nan ne majalisar ta amince da karatu na farko na dokar, yayin da a Larabar nan kuma ta tsallake karatu na biyu da na uku, bayan zaman sirri da majalisar ta yi ta tabbatar da sahale gyararrakin da aka yi mata.
shugaban masu rinjaye na majalisar Alhaji Labaran Abdul Madari ya ce, “sassan da aka yiwa gyara a yanzu sun hadar da sashi na biyu da sashi na 22 da 23 zuwa 50”
Tun da fari dai gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya aikewa majalisar buƙatar yiwa wasu sassan dokar gyara, inda kuma bayan nazari da bincike tare da zama na musamman da majalisar ta yi ta kammala aikinta.
A zaman na yau majalisar ta karɓi wata wasiƙa daga ma’aikatar ƙananan hukumomi da ta aiko da sunayen mutanen da take buƙatar majalisar ta tantance su domin naɗa su a muƙamin sakatarorin mulki a Ƙananan hukumomin jihar nan 44.
Sai sai bayan da shugaban majalisar Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari ya kammala karanta wasiƙar ne sai ya sanar da kwamitoci 6 da za su yi aikin tantancewar tare da basu Mao guda domin su gabatar da rahotonsu.
You must be logged in to post a comment Login