Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majalisar dokokin Kano ta amince wa Abba Kabir ya naɗa masu ba shi shawara 20

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da buƙatar da Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ya miƙa gabanta ta neman ta sahale masa ya naɗa mutane 20 a matsayin masu ba shi shawara.

Tun da fari gwamnan ya buƙaci hakan ne ta cikin wata wasiƙa da ya aike wa majalisar wadda shugabanta Jibrin Isma’il Falgore, ya karanta ta a zaman majalisar na yau Laraba.

Ta cikin wasiƙar, gwamnan ya buƙaci naɗin nasu ne domin samun gudanar da mulkin Kano yadda ya dace kamar yadda shugaban majalisar ya karanta.A nasa ɓangaren, shugaban masu rinjaye na majalisar Alhaji Lawan Hussaini mai wakiltar ƙaramar hukumar Dala, ya yi ƙarin haske kan dokar da ta bai wa gwamnan damar naɗa irin waɗannan muƙamai.

Gabanin fara zaman majalisar, ta rantsar da Yusuf Bello Aliyu, mai wakiltar ƙaramar hukumar Nassarawa a matsayin ɗan majalisa sakamakon rashin rantsar da shi a jiya Talata.

 

Rahoton: Auwal Hassan Fagge

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!