Labarai
Majalisar dokokin Kano ta buƙaci gwamnati ta samar da Ruwa a Dawakin Kudu
Majalisar dokokin jihar Kano, ta buƙaci gwamnatin jihar Kano da ta samar da ruwan sha daga matatar ruwa ta Tamburawa ga al’ummar Mazaɓar Dawaki da Ƴan Barau da Ɗosan da yankunan Gurjiya da kuma Tsakuwa da Yankaba Tsari da mazaɓar Unguwar Duniya duk a ƙaramar hukumar Dawakin Kudu.
Majalisar ta buƙaci hakan ne bisa ƙudurin da wakilin ƙaramar hukumar Dawakin Kudu Shu’aibu Rabi’u ya gabatar a zamanta na yau Laraba.
Da ya ke gabatar da ƙudurin, ɗan majalisar ya ce, mazauna yankunan na fuskantar matsalolin rashin ruwa.
A gudunmawar da ya bayar dangane da ƙudurin, ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Ƙaraye Injiniya Ahmed Ibrahim Karaye, ya bayyana Damuwa bisa yadda yankuna da dama musamman na karkara ke fama da ƙamfar ruwan amfanin yau da kullum.
You must be logged in to post a comment Login