Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majalisar dokokin Kano ta musanta karɓar toshiyar baki wajen rushe Masarautu

Published

on

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta musanta wani labari da ke yawo a shafukan sada zumunta dake cewar an bai wa mambobinta kudade da Motocin Don yin amfanin da Dokoki wajen rushe masarautun Jihar Kano.

Shugaban majalisar Alhaji Jibril Isma’il Falgore, ne ya bayana haka ta bakin Mai magana da yawunsa Kamaluddin Sani Shawai, ya na mai bayyana matsayar majalisar na daukar mataki kan ƙafar da ta wallafa jita-jitar.

Kamaluddin Sani, ya kuma bukaci mutane su yi watsi da labarin da ake yadawa kan yan majalisar a baya-bayan nan.

ya kuma Kara da cewar majalisar za ta ci gaba da gudanar da aikinta bisa tsarin doka tare da buƙatar mujallar da ta yada labarin da ta janye ko majalisar ta daukin matakin doka.

Majalisar dokokin ta kuma buƙaci al’ummar Jihar Kano su ci gaba da zama lafiya tare da kauce wa yada jita-jita.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!