Labarai
Majalisar dokokin Kano za ta kammala aiki kan kasafin 2022 kafin ƙarshen 2021
Majalisar dokokin jihar Kano, ta ce kafin ƙarshen shekarar 2021 za ta kammala aiki kan kasafin baɗi da Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar mata.
Shugaban majalisar Engr Hamisu Ibrahim Chidari, ne ya bayyana hakan a zaman majalisar na yau, bayan da Gwamnan ya gabatar da kasafin na fiye da Naira biliyan 196.
Chidari ya ce, majalisar za ta yi hakan ne domin ganin an fara amfani da kasafin a farkon shekarar 2022.
Kasafin 2022: Ganduje ya gabatar da naira biliyan 196 ga majalisar dokoki
Haka kuma ya buƙaci ɓangarorin tattara harajin jihar Kano da su ƙara ƙaimi wajen samun nasarar tara kuɗaɗen da gwamnatin ke yunƙurin samu.
Chidari ya kuma taya Gwamnatin jihar Kano murna kan irin nasarorin da ta samu wajen gudanar da ayyukanta na kasafin kuɗin bana.
Shugaban majalisar ya kuma buƙaci ƙungiyoyi masu zaman kansu da masu kishin al’umma da su shirya amsa goron gayyatar majalisar kamar yadda ta saba domin bada gudunmawarsu kafin amincewa da kasafin na baɗi.
A ganawarsa da manema labarai bayan gabatar da kasafin, gwamna Ganduje ya sha alwashin ganin gwamnatinsa ta aiwatar da dukkanin ayyukan da ta sanya a cikin kasafin.
A zaman na ranar Alhamsi akawun majalisar Garba Baƙo Gezawa, ya gabatar da karatu na ɗaya ga dokar Kotun sulhu ta shekarar 2021 da karatu na ɗaya na dokar ayyukan Kotunan Majistare da aikin Lauyoyi ta shekarar 2021.
You must be logged in to post a comment Login