Labarai
Majalisar dokokin Rivers ta buƙaci gwamna Fubara ya gabatar da kasafi da sunayen sabbin kwamishinoni

Majalisar dokokin jihar Rivers ta buƙaci gwamnan jihar Similanayi Fubara ya aike mata da sunayen mutanen da yake son naɗawa a muƙamn kwamishinoni domin ta amince da su.
Ƴan majalisar ƙarƙashin jagorancin shugabanta Martin Amaewhule, sun bayyana hakan ne a lokacin da suka koma aiki daga dakatarwar wata shida da shugaba Tinubu ya yi musu bayan sanya dokar ta-ɓaci a jihar cikin watan Maris.
Rahotonni daga jihar sun nuna cewa, ya zuwa yanzu gwamnan jihar da kuma mataimakiyarsa ba su shiga ofishinsu ba.
You must be logged in to post a comment Login