Labarai
NDLEA ta cafke wasu ababen fashewa a hanyar zuwa Zamfara

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA ta ce, ta kama wasu abubuwan fashewa a kan hanyar zuwa jihar Zamfara da aka yi niyyar shigar da su.
Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a karshen mako.
Ta ce, jami’an ta da ke aikin sintiri a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya ne suka kama wata mota wadda ke dauke da abubuwan fashewan bayan da ta tashi daga jihar Nasarawa zuwa Zamfara.
NDLEA ta ce, binciken da suka yi game da motar ne ya kai suka gano abubuwan fashewar har guda 942 a daure a cikin buhu tare da kama wani da ake zargi mai suna Nura Sani dan kimanin shekaru 30.
Haka kuma Shugaban hukumar Janar Buba Marwa mai ritaya, ya bayar da umarnin tsare mutumin da ake zargi da kuma abubuwan da aka gano a wurinsa, don ci gaba da bincike.
You must be logged in to post a comment Login