Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majalisar gudanarwar hukumar NHIS ta yi barazanar murabus

Published

on

Majalisar gudanarwar hukumar inshorar lafiya ta kasa NHIS ta yi barazanar murabus matukar fadar shugaban kasa ta dakile matakin majalisar na dakatar shugaban hukumar Farfesa Usman Yusuf.

Su ma kamfanonin da ke bayar da Inshorar tabakin wakilinsu Dokta Lekan Ewenla sun bukaci Farfesa Usman Yusuf din ya tsame su daga cikin sabanin dake tsakaninsa da Majalisar gudanarwar.

A ranar alhamis din da ta gabata ne majalisar gudanarwar ta dagatar da Farfesa Usman Yusuf daga mukaminsa har sai baba ta gani, karo na biyu kenan a cikin watanni 15 da suka gabata, bisa zargin almundahana.

Sai dai shugaban hukumar ta NHIS ya ce majalisar gudanarwar ba ta da hurumin dakatar da shi, illa shugaban Muhammadu Buhari da ya nada shi, a don haka ba zai martaba hukuncin na su ba.

A jiya dai Majalisar Wakilai ta baiwa Kwamitocinta na harkokin Lafiya da tabbatar da bin ka’idar aiki su bibiyi lamarin tare da gudanar da cikakken bincike a kai.

Masahwarcin shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya sanar da cewa matakin Majalisar gudanarwar ya saba ka’ida, kuma gwamnatin tarayya na iya kokarinta don warware matsalar, inda Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ke ganawa da hukumomin da suka dace don kawo karshen matsalar.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!