Connect with us

Labaran Kano

‘Yan Najeriya 186 ne aka kwaso daga kasar Afrika ta Kudu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta kwaso wasu ‘yan kasar nan mazauna Afirka ta kudu su 186 wadanda suka makale acan sakamakon cutar corona.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun ministan harkokin kasashen wajen kasar nan Sarah Sanda, ta ce jirgin ‘yan Najeriyar ya bar filin jirgin saman Tambo da ke birnin Johannesburg da misalin kare hudu da rabi agogon kasar ta afurka ta kudu a yau Alhamis.

Ya zuwa yanzu dai acewarta jimillar ‘yan NAJERIYA dubu goma ne wadanda aka rufe kofa da su a wasu kasashen duniya sakamakon cutar covid-19 aka dawo da su gida.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!