Labarai
Majalisar Kano ta amince Ganduje ya ciyo bashin Naira Biliyan Goma Sha Biyar
Majalisar dokokin jihar Kano ta amince kananan hukumomin jihar arba’in da hudu da su ciyo bashin Naira Biliyan Goma Sha Biyar domin da shirin ba da ilimi kyauta da gwamnatin jihar ta kaddamar a shekarar da ta gabata.
Hakan ya biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin kula da kananan hukumomi wanda dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Kiru, Kabiru Hassan Dashi, ya gabatar a yau.
Da ya ke zantawa da manema labarai bayan kammala zaman majalisar, Kabiru Hassan Dashi, wanda Kuma shine mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar, ya ce, kudaden za su taimakawa kananan hukumomin wajen aiwatar da shirin ba da ilimi kyauta da gwamnatin Kano ta aiwatar a bara.
“Yanzu kananan hukumomin za su iya gina sababbin ajujuwa da sayan kayayyakin sawa na dalibai saboda samun kudaden”Inji Kabiru Hassan Dashi.
A shekaran jiya litinin ne gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya turo da wasikar da ya bukaci majalisar ta amince don kananan hukumomi su ciyo bashin naira miliyan dari uku da arba’in Kowannensu, don aiwatar da shirin ba da ilimi kyauta.