Connect with us

Labarai

Majalisar Kolin Shari’ar Musulunci ta bayyana damuwa kan kalaman Rabaran Ezekiel

Published

on

Majalisar Koli ta Shari’ar addinin musulunci  ta kasa ta bayyana damuwa kan wasu kalamai da wani malamin Coci, Rabaran  Ezekiel Dachomo, ya yi, da ta ce maganganun na kunshe da sakonnin rura rikicin addini da zarge-zarge kan Musulunci da al’ummar Musulmi a kasar nan. 

 

Ta cikin wata sanarwa da Sakatare Janar na Majalisar, Nafiu Baba Ahmad, Mni, ya sanya wa hannu, ta bukaci hukumomin tsaro su binciki batun tare da ɗaukar matakin doka kan duk wanda aka samu da laifi.

 

Majalisar ta ce a lokacin da kasar nan ke fama da matsalolin tsaro kamar ta’addanci, fashi da makami da garkuwa da mutane, bai dace wasu su riƙa yin kalaman da za su haddasa rashin jituwa tsakanin al’umma ba.

 

Ta kuma jaddada cewa addinin Musulunci yana koyar da zaman lafiya da girmama rayuwar ɗan Adam, tare da kira ga shugabannin addinai na Musulmi da Kirista su haɗa kai wajen yin Allah wadai da kalaman da ke haifar da ƙiyayya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!