Labarai
Majalisar malamai ta Kano ta sake jaddada mubaya’arta ga Sheikh Ibrahim Khalil
Majalisar malamai ta jihar Kano ta sake jaddada mubaya’arta ga Sheikh Ibrahim Khalil a matsayin shugaban majalisar.
Yayin wani taro da majalisar ta gudanar a ranar Talata da shugabanninta ta yi Allah wadai kan yunƙurin da wasu da ba ƴaƴan majalisar ba suka yi na bada sanarwar tsige Malamin.
Farfesa Muhammad Babangida Muhammad shi ne mataimakin sakataren majalisar ya ce “An kafa wannan majalisar a shekara ta 1981 amma akwai wadanda ba su taɓa halartar taron majalissar ba, kuma har kawo yanzu waɗanda suka fitar da wannan sanarwa sun kasa bayyana kan su, a matsayinsu na ƴan cikin majalisar, sai dai mun fahimci suna son tayar da ƙura a majalissar”.
“Abin takaici ne ace wasu ƴan tsirarun malamai su ayyana wani sabon shugaba a majalisar, a don haka muna jadda mubaya’ar mu ga Malam Khalil a matsayin shugaba, kuma muna kiran sa ya ƙara kan jajircewar da yake akan shugabancin majalissar.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan da wani tsagi a majalisar ya ayyana tsige Malam Ibrahim Khalili a matsayain shugaban majalisar.
You must be logged in to post a comment Login