Labarai
Majalisar rabon tattalin arziki ta amince kashe Biliyan 100 wajen gyaran cibiyoyin horas da jami’an tsaro

Majalisar rabon tattalin arzikin kasa ta Najeriya ta amince da naira biliyan 100, domin gyaran cibiyoyin horas da ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro a faɗin kasar.
An dauki wannan matakin ne a taron majalisar na 154, wanda aka gudanar ta intanet, bayan gabatar da rahoton kwamitin wucin-gadi da aka kafa domin tantance halin da cibiyoyin horaswa na jami’an tsaro ke ciki.
Majalisar ta kuma amince da Naira 2.6 biliyan domin biyan kudin masu ba da shawara kan aikin.
Sai dai duka waɗannan kuɗaɗen da aka amince sai sun jira amincewar shugaban ƙasa kafin a fitar da su.
Tun a taron majalisar zartaswa watau NEC na 152 a watan Oktoba Shugaba Tinubu ya bayar da shawarar fara gagarumin gyara da sabunta cibiyoyin horaswa na jami’an tsaro a fadin ƙasa.
You must be logged in to post a comment Login