Labarai
Majalisar sarakuna : Ganduje ya bada umarnin da a gyara gidan Shattima
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya baiwa Kwamishinan ayyuka da cigaba Injiniya Mu’azu Magaji umarnin da a gyara gidan tarihi na Shattima a matsayin ofishin majalisar masarautun gargajiya ta jihar Kano, duk da umarnin kotu na dakatar da sabuwar dokar majalisar masarautar Kano.
Gidan Shattima dai na kusa da fadar maimartaba sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II.
Wannan nakunshe cikin sanarwar da sakataren yada labaran gwamna Abba Anwar ya fitar cewa gwamnan ya yanke shawarar yin hakan a wani matakin na shirye-shiryen kaddamar da sabuwar majalisar masarautar Kano.
Gwamna Ganduje ya nada Sarkin Kano Muhammad Sunusi shugaban majalisar Sarakunan Jihar Kano
Ganduje da Sarkin Kano sun gana da masu zuba jari daga kasar China
Ina rokon Ganduje ya rushe shirinsa na rarraba masarauta -Sheikh Dahiru Bauchi
A cewar sanarwar umarnin gyaran gidan Shattima na nuna cewar na nuna cewar nan bada jimawa za’a kaddamar da sabuwar majalisar masarautar Kano wanda yayi dai-dai da dokar data kafa majalisar sarakunan yanka ta jihar Kano wanda majalisar dokoki ta jihar Kano ta zartar a kwanakin baya.